TAKAITACCEN TARIHIN KI?
Sunana maimuna abubakar wacce aka fi sani da momi gombe actress a matsana’antar kannywood, an haife ni a garin gombe anan nayi primary
school dina anan nayi secondary school dina, dukkanin rayuwata a garin gombe nayi, sai yanzu kuma sana’a ta maida ni garin kano.
YA AKA YI KIKA SAMU SUNA MOMI?
Momi suna ne da na gada a wajen kakata maman baba na, ana kiranta maimunatu to su kuma baza su iya kiran sunan ba, shi yasa baba na yake kira na maimunatu.
KI BAMU LABARIN YADDA KIKA SHIGA KANNYWOOD?
Ta hannun mai gida na Usman Mu’azu na shiga Film, usman ya kasance dan garin Gombe ne kuma yana zuwa har cikin gidan mu, kuma yasan yan uwana, iyaye na da kakanne na, kuma ya zama kamar dan gida, a lokacin ni kuma ina sha’awar yin Film, idan suna aikin su na film, a gida ana saka ni na kai musu abinci, idan na kai abincin sai na zauna nayi ta kallon su, sai watarana nace masa ina so nima na shiga masana’antar kannywood, sai yace ai iyaye na baza su barni ba, sai nace idan kayi musu magana ai zasu barni, da ya lura ina so film sosai, sai yayi magana da mama ta kuma sai ta barni na fara film.
A WANNE FILM KIKA FARA FITOWA ?
Na fara fitowa ne a wani film mai suna sunan ka.
ME YASA AKA FI GANIN KI A BIDIYON WAKOKI?
Kasan kowa da yadda yake, aikin ne yazo da haka
AINA KIKA KOYI RAWA?
Ban koyi rawa a ko ina ba, kawai idan aka ce nayi rawa sai naga ina yi.
KE CE JARUMAR MATA DA HAMISU BREAKER YA YI WAKA DA KE?