Babbar jarumar kannywood rahama sadau ta bayyana wa duniya a shekarun baya kafin ta shiga harkar fim an bata yi mata fyade. Sannan ta bayyana yadda akayi mata fyaden.
Ta bayyana hakane a kwanan baya jaruma Rahama sadau taba masoyan ta dama suyi mata kowace tambaya inda wani ya jefe ta da tambayar ko ita budurwa ce.
Rahama sadau ta amsa da wannan amsa wacce ta zama abin cece kuce na tsawon lokaci duba da kasancewar ta budurwa da bata taba aure a yanzu rahama ta fayyace gaskiya.
A wata hira da akayi da ita ta bada labarin ta kamar haka: “Gaskiya ni ba cikakkar budurwa bace. Domin bani da tabbas akan haka.”
“Kuma yana da kyau idan za ka fadi abu to ka kasance kana da tabbas akan shi. A iya sanin da nayi an taba kwanciya da ni. Amma ba’a son raina ba.” Yadda abun ya faru shine:
“Akwai wata rana ina tafiya a cikin dare da niyar zuwa gidan wata kawata sai aka tare ni ina cikin mota, sai suka watsa min wani abu kamar hoda daga nan ban san inda kai na yake ba.”
“An dauki tsawon lokaci sai na gan ni cikin najasa, a bayan gidan wani Alhaji. Nayi kuka sosai har da hawaye domin nasan a dauke min budurci na. Dan haka ni yanzu ba budurwa bace.”
Wannan itace amsar da jarumar ta bada wacce ta janyo mata tsangwama a wajen mutane. Domin Allah ya rufa mata asiri amma ita ta tonawa kan ta