Yadda zaku hada maganin karin Kuzari da Karfi a lokacin saduwa da iyali
👇👇👇👇
Har ila yau dai akwai mutanen da suke fama da
rashin karfi da kuzarin a lokacin da suke saduwa da
iyalinsu, wanda hakan yake haifar musu da
damuwa.
To a yau dai munzo muku da wani ingancaccan
hadin maganin karin kuzari wanda mai irin wannan
matsala zai sami waraka insha Allahu.
Babu makawa bincike ya nuna amfanin da
Tafarnuwa da Citta suke dauke da shi ta bangaren
taimakawa karfi ga
Namiji.
Domin suna dauke da sinadarin dake
taimakawa jiki wajen samun cikkaken kuzari.
Da farko za'a sami Citta danya mai ashar
kamar guda 1 babba, sai a bare bawon dake bayan
ta.
Sannan a samu Tafarnuwa guda daya a bare a debi
sili kamar 3 sai a hada da Cittar a daka a turmi, a
kawo ruwa kofi daya a zuba a ciki a barshi na
tsawon minti 15 sannan a kawo zuma kamar
chokali 4 a zuba a juya sosai asha.
ldan kunyi wannan hadin maganin kun sha sai ku
dauki kamar tsawon minti 30 kafin a kwanta barci,
amma kasha bayan kaci abinci.