Alhamdulillah! Abba ya yiwa Gawuna mugun kaye Rarara yayi kwantan waka/Kwankwaso har ya karaya

 

A ranar litinin ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Abba gida-gida a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

Ga abu takwas da ya kamata ku sani a kansa:

An haife shi ranar 5 ga watan January, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.
Ya yi karatun Firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun Sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.
Abba ya yi karatun difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.
Ya yi karatun digirinsa na biyu digiri a jam’iyyar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.
Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso.
Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.
Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.
Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a ranar 20 ga watan Maris na 2023.