Wata Matashiya yar arewacin na Najeriya mai suna Fatima Sheka ta ce da ta auri talaka Gara ta mutu ba tayi aure ba. Matashiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.
Jarumar tayi wallafa kamar haka “Nifa Idan Har Talaka Zan Aura, To Gwara Na Mutu Ban Yi Auren Ba” a Cewar Fatima Sheka.

Sai dai babu wuya da fadin hakan da tayi masu amfani da dhafin Facebook suka sakata a gaba, wasu suna ganin ai hakan da ta fada ra’ayin ta ne ba nawani ba, a yayin da wasu kuma banda zagi da tsinuwa babu abunda sukeyi.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan wallafar a shafukan sada zumunta ba, musanman wajen yan matan Arewacin Najeriya