Duk wanda baya iya jima’i minti 30 yake saurin kawowa to ga magani



 Maganin saurin kawowa, girman gaba maganin karfin maza da kankancewar gaba.

Ba shakka lallai wannan fa’ida ta kuke karantawa fa’ida ce wacce Al’umma da dama sukai amfani da ita kuma tayi musu tasiri wajen maganin shaanin daya shafi jima’i.

Wannan fa’ida tana kara Sha’awa sannan tana kara ruwan maniy tana maganin saurarin Inzali tana karawa namiji shaawa da kuzari da nishadi da jin dadi a lokacin saduwa da iyali.

Abubuwan da zaka samo domin hadawa sune abubuwa kamar haka.

1. Ganyen kuka.

2. Citta.

3. Kanunfari.

4. Tafarnuwa.

Da farko zaa samu ganyen kuka guda 5 a shanya ya bushe a inuwa,sannan a samu garin citta karamin chokali Garin Tafarnuwa karanin chokali kanunfari chokali 1.

Za’a hade su waje daya a dake su sosai,sai a rika diban rabin karamin chokali ana zubawa a ruwan shayi ba madara ana sha da safe da dare minti 30 kafin a kusanci iyali.

Za’ai wannan hadin na tsawon sati 1 insha Allah za’a samu kuzari karfi da kuma dadewa ana jima’i da rashin saurin kwanciyar gaba.

MAGANIN SANYI KOWANNE IRI CIKIN SAUKI.

Kamar yadda muka kawo muku yadda zaa hada maganin sanyi a baya,a yau ma wata faida wacce take maganin sanyi ma jiki dana mara.

ZA’A SAMO.

1. Furen Zugale.

2. Albasa.

Za’a samu furen Zogale a wanke sai a samu Albasa a yayyanka a hada da furen a dafa,idan aka sauke ya wuce sai a rika sha kamar shayi safe da yamma.

Tsawon sati guda, Allah yasa mu dace.