Jama'a sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum mai shekaru da ya yi wuff da wata kyakkyawar budurwa
An dai gano angon wanda ya cika da farin ciki yana yaye lullubin da aka yi wa amaryar tasa wanda ke nuna ana budar kai ne Sai dai mutane da dama suna ganin sam wannan hadin bai yi ba duba da tazarar shekaru da ke tsakaninsu
⚫ Jama'a a soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da hoto da bidiyon wasu ma'aurata sabbin aure.
• Angon wanda shekaru suka dan fara ja masa ya yi wuff da wata tsaleliyar budurwa danya shakaf.
Tazarar shekaru da ke tsakanin sabbin ma'auratan shine abun da ya fi jan hankalin jama'a zuwa wurinsu inda sam wannan al'amari bai yi wa wasu dadi ba.
Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Amaryarsa Suka Ta Da Kura a Soshiyal Midiya Hoto: hausaa_fulanii Asali:
Instagram A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya kuma shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram ya nuno inda ango ke bude kan amaryarsa cike da farin ciki da zumudi.
Mutane da dama sun ce a ganin farko da suka yi wa hoton, sun zata uba ne da 'yarsa suke bankwana yayin da za a kaita dakin aurenta sai dai labari ya sha banban duba ga yanayin abubuwan da suka faru a bidiyon.
Legit.ng Hausa ta zakulo wasu daga cikin martanonin da jama'a suka yi a kan wannan aure a kasa: sadia_nas ta yi martani: "Masu cewa ai aure ne, sunnah aka raya ya fi a kama ta a hotel,
ku dubi yarinyar nan ku dubi shekarun mutumin nan me yasa bai samo bazawara ba ko wata babbar mace? ko wadda Mijinta ya mutu? ku gaya ma ni a gidan Ubanwa su ka dace?? Wallahi ku ji tsoron Allah, ko a musulunci akwai inda a ke gargadi akan irin wannan auren...a ina zai iya da yarinyar nan? don dai shi namiji kullum a rayuwa shi a ke favoring? comment kuma sai mun yi, wanda ya ce a yi posting a social media."