Innalillahi.. Allah Ya Yi Wa Jarumi Awarwasa Na Shirin Aduniya Rasuwa

 

Allah ya yiwa jarumin fina-finan Hausa Awarwasa rasuwa a yammacin yau bayan fama da gajeriyar rashin lafiya. Jarumin yana fitowa a cikin shiri mai dogon Zango na Aduniya...

Fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Lawan Ahmad shine wanda ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook, Kamar Yadda rahotanni suka nuna Abdulwahab ya rasu ne bayan yasha fama da rashin lafiya ya kuma rasu ne a garin Jos.