Jarumar Wasan Kwaikwayo A Faransa Ta Musulunta

 

Cikin wani labari mai daɗin ji, wata fitacciyar jarumar wasan talabijin na musamman ƴar ƙasar Faransa Marin El Himer, ta karɓi addinin musulunci inda kuma ta bayyana cewa waɗannan kwanaki da ta karɓi musulunci sun zamar mata mafi farin ciki a rayuwarta.

Kwana biyu bayan da ta karɓi addinin Musulunci, Eli Himer ta ɗora wasu hotunta a shafinta na Instagram sanye cikin hijabi a kusa da ɗakin ka’aba, guri mafi tsarki a musulunci.

Yadda ta nuna farin ciki

Ta bayyana tsananin matuƙar farin cikin ta da wannan babban abu da ya sameta na karɓar addinin musulunci, domin tana fatan ta samu rayuwa mai kyau da zata ci gaba da yi mata jagora har ƙarshen rayuwar ta, kamar yadda Shafin internet na Labarun Hausa ya wallafa.