MATASHI YA MUTU YANA KALLON BLUE FILM WATO FIM ƊIN BATSA. LABARI MAI BAN TSORO DA TAUSAYI.


 MATASHI YA MUTU YANA KALLON BLUE FILM WATO FIM ƊIN BATSA.


LABARI MAI BAN TSORO DA TAUSAYI.


Wani Matashi ya shiga ɗakinsa ya kulle ƙofar sai ya kunna fim ɗin batsa a wayarsa yana kallo har ya cire tufafinsa yayi tsirara haihuwar uwarsa.


Mahaifinsa yaji an kira sallah ya shirya zashi masallaci ya biyo ta ƙofar ɗakinsa wane wane tashi kaje kayi sallah Shiru har ya gaji ya tafi masallaci.


Ashe ya shagalta da kallon blue firm yana tsaka da wannan kallo Kwatsam sai heart attack ya kamashi wato ciwon zuciya Mai tsanani ya ringa ihu wayyo zuciyata wayyo zuciyata wayyo zuciyata nan take mahaifiyarsa  tazo ƙofar ɗakinsa tace wane wane ka buɗe ƙofar saide adaidai lokacin Bazai iya Komai ba sai ta Fara kururuwa nan de maƙwafta da Mutanen anguwa suka cika gidan  maƙil sukace da ita meyafaru tace ɗana ne yaketa ihu a ɗaki bayida lafiya Kuma ƙofar a kulle


Nan makota da Mutanen anguwa sukayi shawarin cewa su ɓalle ƙofar ɗakin haka akayi Nan take suka ɓalle saiko suka ga tashin hankali ga Matashin nan tsirara haihuwar uwarsa ga wayarsa tana buɗe yana kallon fim ɗin batsa a wannan hali ya mutu wato yayi mummunar ƙarshe


Ashe kaima bakada lasisin lokacin mutuwa ako Wani hali zaka iya mutuwa shin menene ribar da kake samu Cikin kallon blue firm (fim ɗin batsa) ..?


•SHAWARA•


Don Allah kaima idan kanayi kaji tsoron Allah ka Dena, kema kiji tsoron haɗuwarki da Allah ki Dena.


Ya Allah ka azurtamu da tuba na gaskiya kafin mutuwar mu.🤲


✍️