VIDEO: "Asarar sama da Naira Miliyan 800 na tafka a gidana da yaran Tsula suka kona" - Rarara

 Fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya bayyana irin muguwar asarar da ya tafka sakamakon kona gidansa da aka yi mawakin ya ce "Ba zan daina fadar sunan Tsula ba saboda tsoron wani ko wata duk da cewa yanzu haka a kiyasin da nayi yaransa sun kwashe tare da kona min kayan gida sama da na Miliyan 800 iya na gida kenan ban gama lissafa asarar da nayi a Ofishin 13-13 ba idan na gama zan sanar” in ji shi..