Yawan mutanen da suka mutu ya kai shida a hatsarin jirgin ƙasa na Legas

 


...

An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum shida, yayin da wasu 71 suka jikkata lokacin da jirgin ƙasa ya buge wata motar bas da safiyar Alhamis a yankin Ikeja da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar agajin gaggauwa ta ƙasa (NEMA), na yankin kudu maso yammacin Najeriya, Ibrahim Farinloye shi ne ya tabbatar da lamarin, inda ya ce mutum 29 suna cikin wani mawuyacin hali.

A baya jami'in ya ce mutum biyu ne, daga bisani kuma aka ce uku ynzu kuma yawan waɗanda suka mutu ɗin ya ƙaru zuwa shida, ko da yake rahotanni na cewa za su iya zarce haka, saboda ana ci gaba da aikin ceto.

Ya ce "mata biyu ma'aikatan gwamnatin jiha da wani namiji ne suka fara rasu."

Motar bas ɗin wadda ta gwamnatin jiha ce na ƙoƙarin tsallaka hanyar jirgin ƙasa ta PWD/Sogunle ne a lokacin da jirgin, wanda ya fito daga Abeokuta zuwa cikin birnin Legas ya yi awon-gaba da ita.

Mai magana da yawun Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Adebayo Taofiq shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ana dai ci gaba da aikin ceto, domin tabbatar da cewa babu sauran wanda abin ya rutsa da shi a maƙale.

Mutane sun rinƙa yaɗa hotunan da suka fito daga wurin da haɗarin ya faru.

Wasu labaran da za ku so ku karanta