Itama tsohuwar jaruma sayyada sadiya Haruna tayi martani mai zafi ga wa’yanda suka yiwa Aisah Humaira wannan abin a filin zabe inda tace wallahi duk wata yar kannywood data goyi bayan wannan abin dan kawai basa ra’ayi daya to bata kishin mace.
Kowa yasa abinda ya faru da wannan jarumar yayin da taje Filin zabe wanda aka samu wasu matasa mararsa kishi sukayi mata halin rashin da’a wanda akayi Allah wadai da wannan abin tunda ta bayyana ra’ayinta akan zabe shikkenan wasu mutane suka kullaceta.
Sayyada sadiya Haruna ta baiwa jarumar hakuri Sannan ta soki wa’yanda sukayi wannan abin kuma tace duk mutanen kirki baza suyiwa mace haka ba.
Mun gode sosai da sosai ku cigaba da bibiyar don samu Labarai Duniya da na Kannywood kasance da katsinablood.com