AL'AJABI: "Hoton Bidiyon Sayyada Fanta Sangare tana Wuridi a tsakiyar Teku ya jawo ce-ce-kuce

 Rahotanni daga ƙasar Guinea na cewa shafukan sada zumunta sun cika da ce-ce-kuce da muhawara bayan ɓullar hoton bidiyon ɗaya daga cikin mabiya ɗariƙar Tijjaniyya mai suna Sayyada Fanta Sangare 


Wacce aka hango a tsakiyar wata babbar madatsar ruwan Teku tana gudanar da Sallar Walaha bayan ta kamma ta zauna tana yin Lazimi lamarin wanda ya faru a arewacin ƙasar ta Guinea ya ja hankalin mutane da dama


A nata ɓangare Sayyada Fanta ta ce "Wannan ba wani babban al'amari bane a wajenta saboda ita da ruwan dukkansu bayin Allah ne, kuma matuƙar mutum zai ji tsoron Allah sannan yayi biyayya ga Allah da MANZONSA kuma ya lizimci Istigfari, Salatin ANNABI da Hailala, Allah zai iya sawa komai ya yi masa biyayya ciki hadda Ruwa da Wuta


Muna fatan Allah ya sa mu cika da


Imani